<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>257</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ina da aiki nan, Allah zan ɗaukaka.
 Raina zan sa a hannunsa a ƃoye a Sama can.

[V2]
 2) Zan yi ta aikina, zan cika kirana.
 Da hannu biyu, da zuciya ɗaya in bauta wa Yesu.

[V3]
 3) Ya Ubangijina, ka ba ni Ruhunka.
 Ka shirya bawanka a nan don aikin Sama can.

[V4]
 4) Ka ba ni taimako, ka ji addu'ata,
 Don kada dai in kasa nan, in rasa ladana.</lyrics>
<title>Ina da Aiki Nan, Allah Zan ɗaukaka LW257</title>
</song>